Littafi Mai Tsarki

A.m. 23:31-35 Littafi Mai Tsarki (HAU)

31. Saboda haka, sojan suka ɗauki Bulus, kamar yadda aka umarce su, suka kai shi Antibatiris da daddare.

32. Kashegari kuma suka bar barade su ci gaba da shi, su kuwa suka koma kagarar soja.

33. Da baraden suka isa Kaisariya, suka ba mai mulkin wasiƙar, suka kai Bulus a gabansa.

34. Da ya karanta wasiƙar, ya tambayi Bulus ko shi mutumin wane lardi ne? Da ya ji daga Kilikiya yake,

35. ya ce, “Zan saurari maganarka duka, in masu ƙararka sun zo.” Sai kuma ya yi umarni a tsare shi a fadar Hirudus.