Littafi Mai Tsarki

A.m. 23:24-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Ya kuma yi umarni su shirya wa Bulus dabbobin da zai hau, don su kai shi wurin mai mulki Filikus lafiya.

25. Ya kuma rubuta wasiƙa kamar haka:

26. “Daga Kalaudiyas Lisiyas zuwa ga mafifici mai mulki Filikus. Gaisuwa mai yawa.

27. Bayan haka mutumin nan, Yahudawa sun kama shi, suna kuma gab da kashe shi, sai na yi farat na je da soja na ƙwato shi, saboda na ji cewa shi Barome ne.

28. Da ina so jin laifin da suke zarginsa a kai, sai na kai shi majalisarsu.

29. Na kuwa tarar suna zarginsa a kan maganar Shari'arsu, amma laifin da suka ɗora masa bai kai ga kisa ko ɗauri ba.

30. Da aka buɗa mini cewa akwai wani makircin da aka ƙulla masa, nan da nan na aika da shi a gare ka, na kuma umarci masu ƙararsa su faɗi ƙararsu a gabanka. Wassalam.”

31. Saboda haka, sojan suka ɗauki Bulus, kamar yadda aka umarce su, suka kai shi Antibatiris da daddare.

32. Kashegari kuma suka bar barade su ci gaba da shi, su kuwa suka koma kagarar soja.

33. Da baraden suka isa Kaisariya, suka ba mai mulkin wasiƙar, suka kai Bulus a gabansa.