Littafi Mai Tsarki

A.m. 21:22-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

22. To, ƙaƙa ke nan? Lalle za su ji labarin zuwanka.

23. Saboda haka sai ka yi abin da za mu faɗa maka. Muna da mutum huɗu da suka ɗauki wa'adi.

24. Sai ka tafi da su ku tsarkaka gaba ɗaya, ka kuma biya musu kome don su samu su yi aski. Ta haka, kowa zai sani duk abin da aka gaya musu game da kai, ba wata gaskiya a ciki, kai kuma kana kiyaye Shari'a.

25. Amma game da al'ummai da suka ba da gaskiya, mun aika da wasiƙa a kan mun hukunta, cewa su guji cin abin da aka yanka wa gunki, da fasikanci, da cin abin da aka maƙure, da kuma cin nama tare da jini.”

26. Sa'an nan Bulus ya ɗibi mutanen nan, kashegari kuma da suka tsarkaka tare, sai ya shiga Haikali domin ya sanar da ranar cikar tsarkakewar tasu, wato ranar da za a ba da sadaka saboda kowannensu.

27. Da kwana bakwai ɗin suka yi kusan cika, Yahudawan ƙasar Asiya suka gan shi a Haikalin, sai suka zuga taron duka, suka danƙe shi,

28. suna ihu suna cewa, “Ya ku 'yan'uwa Isra'ilawa, ku taimaka! Ga mutumin da yake bi ko'ina yana koya wa mutane su raina jama'armu da Shari'a, da kuma wannan wuri. Banda haka kuma har ma ya kawo al'ummai a cikin Haikalin, ya ƙazantar da wurin nan tsattsarka.”

29. Don dā ma can sun ga Tarofimas Ba'afise tare da shi a cikin gari, sun kuma zaci Bulus ya kawo shi Haikalin.

30. Sai duk garin ya ruɗe, jama'a suka ɗungumo a guje suka danƙe Bulus, suka ja shi waje daga Haikalin, nan da nan kuma aka rufe ƙofofi.