Littafi Mai Tsarki

A.m. 2:7-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Sai suka yi al'ajabi suka yi mamaki, suna cewa, “Ashe, duk masu maganar nan ba Galilawa ba ne?

8. Ƙaƙa kuwa ko wannenmu yake ji da bakin garinsu ake magana?

9. Ga mu kuwa, Fartiyawa, da Madayanawa, da Elamawa, da mutanen ƙasar Bagadaza, da na Yahudiya, da na Kafadokiya, da na Fantas, da na Asiya,

10. da na Firijiya, da na Bamfiliya, da na Masar, da kuma na kewayen Kurane ta ƙasar Libiya, har ma da baƙi daga Roma, wato Yahudawa, da kuma waɗanda suka shiga Yahudanci,

11. da kuma Karitawa, da Larabawa, duk muna ji suna maganar manyan al'amuran Allah da bakunan garuruwanmu.”

12. Duk kuwa suka yi mamaki, suka ruɗe, suna ce wa juna, “Me ke nan kuma?”