Littafi Mai Tsarki

A.m. 18:19-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Sai suka isa Afisa, a can ne kuma ya bar su, shi kuwa ya shiga majami'a ya yi muhawwara da Yahudawa.

20. Sai suka roƙe shi ya ƙara jimawa a wurinsu, amma bai yarda ba.

21. Sai dai ya yi bankwana da su, ya ce, “Zan dawo wurinku in Allah ya so.” Sa'an nan ya tashi daga Afisa a jirgin ruwa.

22. Da ya sauka a Kaisariya, sai ya je Urushalima, ya gaisa da Ikkilisiya, sa'an nan ya tafi Antakiya.

23. Bayan da ya ɗan jima a nan, ya tashi ya zazzaga ƙasar Galatiya da ta Firijiya, yana bin gari gari, yana ƙarfafa dukan masu bi.

24. To, wani Bayahude mai suna Afolos ya zo Afisa. Shi kuwa asalinsa mutumin Iskandariya ne, masani ne kuwa, ya san Littattafai ƙwarai da gaske.

25. An karantar da shi tafarkin Ubangiji, da yake kuma muhimmanci ne ƙwarai, yakan yi ta magana kan al'amuran Yesu, yana kuma koyar da su sosai, amma fa baftismar Yahaya kaɗai ya sani.