Littafi Mai Tsarki

A.m. 10:2-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Shi kuwa mutum ne mai ibada, yana tsoron Allah shi da iyalinsa duka, yana yana ba jama'a sadaka hanu sake, yana kuma addu'a ga Allah a kai a kai.

3. Wata rana wajen ƙarfe uku na yamma, ya ga wani mala'ikan Allah a fili cikin wahayi, ya shigo, ya ce masa, “Ya Karniliyas.”

4. Shi kuwa ya zura masa ido a tsorace, ya ce, “Ya Ubangiji, mene ne?” Mala'ikan kuma ya ce masa, “Addu'arka da sadakarka sun kai har a gaban Allah, abubuwan tunawa ne kuma a gare shi.

5. To, yanzu, sai ka aiki mutane Yafa su kirawo Saminu, wanda ake kira Bitrus,

6. ya sauka a gun Saminu majemi, wanda gidansa yake a bakin bahar.”

7. Da mala'ikan da ya yi masa magana ya tafi, ya kira barorinsa biyu, da kuma wani soja mai ibada daga cikin waɗanda suke yi masa hidima kullum.

8. Da ya ba su labarin kome, ya aike su Yafa.

9. Kashegari suna cikin tafiya, sun zo kusa da gari ke nan, sai Bitrus ya hau kan soro yin addu'a, wajen rana tsaka.

10. Yunwa ta kama shi, har ya so ya ci wani abu. Ana cikin shirya abincin, sai wahayi ya zo masa,

11. ya ga sama ta dare, wani abu kuma yana saukowa kamar babban mayafi, ana zuro shi ƙasa ta kusurwoyinsa huɗu.

12. Cikinsa akwai kowace irin dabba, da masu jan ciki, da tsuntsaye.

13. Sai ya ji wata murya ta ce masa, “Bitrus, tashi, ka yanka ka ci.”

14. Amma Bitrus ya ce, “A'a, ya Ubangiji, don ban taɓa cin wani abu marar tsarki ko mai ƙazanta ba.”