Littafi Mai Tsarki

A.m. 10:15-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Sai ya sāke jin murya, ji na biyu, ta ce, “Abin da Allah ya tsarkake, kada ka ce da shi marar tsarki.”

16. Da an yi wannan sau uku, nan da nan aka yi sama da abin.

17. Bitrus na a cikin damuwa ƙwarai a kan ko mece ce ma'anar wahayin da aka yi masa, sai ga mutanen da Karniliyas ya aiko tsaye a ƙofar zaure, sun riga sun tambayi gidan Saminu,

18. suna sallama, suna tambaya ko Saminu da ake kira Bitrus a nan ya sauka.

19. Tun Bitrus yana bibiya wahayin nan, Ruhu ya ce masa, “Ga mutum uku nan suna nemanka.

20. Tashi, ka sauka, ku tafi tare, ba da wata shakka ba, domin ni ne na aiko su.”

21. Sai Bitrus ya sauka wurin mutanen, ya ce musu, “Ga ni, ni ne kuke nema. Wace magana yake tafe da ku?”