Littafi Mai Tsarki

A.m. 1:8-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Amma za ku sami iko sa'ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauko muku, za ku kuma zama shaiduna a Urushalima, da duk ƙasar Yahudiya, da ta Samariya, har ya zuwa iyakar duniya.”

9. Da ya faɗi haka, suna cikin dubawa, sai aka ɗauke shi Sama, wani gajimare ya tafi da shi, ba su ƙara ganinsa ba.

10. Suna cikin zuba ido sama, shi kuma yana tafiya, sai ga mutum biyu tsaye kusa da su, saye da fararen tufafi.

11. Sai suka ce, “Ya ku mutanen Galili, don me kuke tsaye kuna duban sama? Yesun nan da aka ɗauke daga gare ku aka kai shi Sama, zai komo ne ta yadda kuka ga tafiyarsa zuwa Sama.”

12. Sai suka koma Urushalima daga dutsen nan da ake kira Dutsen Zaitun, wanda yake kusa da Urushalima, wajen mil ɗaya.

13. Da suka shiga birnin, suka hau soro inda suke zama, wato Bitrus, da Yahaya, da Yakubu, da Andarawas, da Filibus, da Toma, da Bartalamawas, da Matiyu, da Yakubu na Halfa, da Saminu Zaloti, da kuma Yahuza na Yakubu.

14. Duk waɗannan da nufi ɗaya suka nace da addu'a, tare da mata, da Maryamu uwar Yesu, da kuma 'yan'uwansa.

15. To, a kwanakin nan Bitrus ya miƙe tsaye cikin 'yan'uwa, (wajen mutum ɗari da ashirin ne a taron), ya ce,

16. “Ya ku 'yan'uwana, lalle ne a cika Nassin nan da Ruhu Mai Tsarki ya faɗa a dā ta bakin Dawuda a game da Yahuza, wanda ya yi wa masu kama Yesu jagaba.

17. Don an lasafta shi cikinmu dā, an kuma ba shi tasa hidima cikin aikin nan.

18. (To, shi mutumin nan, da ladan mugun aikinsa ya sayi wani fili, sai ya fāɗi da kā, cikinsa ya fashe, kayan cikinsa duk suka zubo.