Littafi Mai Tsarki

A.m. 1:24-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Sai suka yi addu'a, suka ce, “Ya Ubangiji, masanin zuciyar kowa, a cikin waɗannan mutum biyu ka nuna wanda ka zaɓa,

25. yă karɓi matsayi cikin aikin nan da manzancin nan da Yahuza ya bauɗe wa, don yă cike gurbinsa.”

26. Sai suka yi musu kuri'a, Matiyas ya ci, aka kuma sa shi a cikin manzannin nan goma sha ɗaya.