Littafi Mai Tsarki

A.m. 1:2-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. har ya zuwa ranar da aka ɗauke shi aka kai shi Sama, bayan ya yi umarni ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzannin da ya zaɓa.

3. Ya bayyana kansa gare su a raye bayan shan wuya tasa, tare da tabbatarwa masu yawa, masu ƙarfi kuma, yana bayyana gare su a kai a kai har kwana arba'in, yana zancen al'amuran Mulkin Allah.

4. Sa'ad da yake tare da su, ya umarce su kada su tashi daga Urushalima, amma su jira cikar alkawarin nan da Uba ya yi, “wanda kuka ji daga bakina,

5. domin Yahaya kam, da ruwa ya yi baftisma, amma kafin 'yan kwanaki da Ruhu Mai Tsarki za a yi muku baftisma.”

6. Saboda haka da suka taru, suka tambaye shi suka ce, “Ya Ubangiji, yanzu ne za ka sāke kafa wa Isra'ila mulki?”

7. Ya ce musu, “Sanin lokatai da zamanai, da Uba ya sa cikin ikonsa, ba naku ba ne.

8. Amma za ku sami iko sa'ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauko muku, za ku kuma zama shaiduna a Urushalima, da duk ƙasar Yahudiya, da ta Samariya, har ya zuwa iyakar duniya.”

9. Da ya faɗi haka, suna cikin dubawa, sai aka ɗauke shi Sama, wani gajimare ya tafi da shi, ba su ƙara ganinsa ba.

10. Suna cikin zuba ido sama, shi kuma yana tafiya, sai ga mutum biyu tsaye kusa da su, saye da fararen tufafi.