Littafi Mai Tsarki

Afi 6:6-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. ba aikin ganin ido ba, kamar masu son faranta wa mutane rai, sai dai kamar bayin Almasihu masu aikata abin da Allah yake so, da zuciya ɗaya,

7. kuna bauta da kyakkyawar niyya domin Ubangiji kuke yi wa, ba mutane ba.

8. Kun sani, kowane alherin da mutum ya yi, ko shi ɗa ne ko bawa, Ubangiji zai sāka masa shi.

9. Ku iyayengiji, ku ma ku yi musu haka, ku bar tsorata su, ku sani, shi wanda yake Ubangijinsu da ku duka, yana Sama, shi kuwa ba ya zaɓe.

10. A ƙarshe kuma, ku ƙarfafa ga Ubangiji, ga ƙarfin ikonsa.

11. Ku yi ɗamara da dukan makamai na Allah, don ku iya dagewa gāba da kissoshin Iblis.

12. Ai, famarmu ba da 'yan adam muke yi ba, amma da mugayen ruhohi ne na sararin sama, masarauta, masu iko, da waɗanda ragamar mulkin zamanin nan mai duhu take hannunsu.

13. Saboda haka, sai ku ɗauki dukan makamai na Allah, domin ku iya dagewa a muguwar ranar nan, bayan kuma kun gama kome duka, ku dage.

14. Saboda haka fa ku dage, gaskiya ta zama ɗamararku, adalci ya zama sulkenku,