Littafi Mai Tsarki

Afi 5:8-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. domin dā ku duhu ne, amma a yanzu ku haske ne a cikin Ubangiji. Ku yi zaman mutanen haske,

9. domin haske shi ne yake haifar duk abin da yake nagari, na adalci, da na gaskiya.

10. Ku dai tabbata abin zai gamshi Ubangiji.

11. Ku yi nesa da ayyukan duhu na banza da wofi, sai dai ku tona su.

12. Gama abin kunya ne a ma faɗi abubuwan da suke yi a asirce.

13. Duk abin da aka kawo a gaban haske a san ainihinsa, gama duk abin da aka san ainihinsa ya haskaka.

14. Saboda haka aka ce,“Farka, ya kai mai barci, ka tashi daga matattu.Almasihu kuwa zai haskaka ka.”

15. Saboda haka, sai ku mai da hankali ƙwarai ga zamanku, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai masu hikima.

16. Ku yi matuƙar amfani da lokaci don kwanaki mugaye ne.

17. Don haka kada ku zama marasa azanci, sai dai ku fahimci abin da yake nufin Ubangiji.

18. Kada kuma ku bugu da giya, hanyar masha'a ke nan. Sai dai ku cika da Ruhu,

19. kuna zance da junanku da kalmomin zabura, da waƙoƙin yabo, da waƙoƙi na ruhu, kuna raira waƙoƙi da zabura ga Ubangiji da yabo a zukatanku.