20. waɗanda aka gina bisa tushen manzanni da annabawa, Almasihu Yesu kansa kuwa shi ne mafificin dutsen ginin,
21. dukan wanda aka haɗa tsarin ginin a cikinsa, yana kuma tashi ya zama haikali tsattsarka na Ubangiji.
22. A cikinsa ne ku kuma aka gina ku, ku zama mazaunin Allah ta wurin Ruhu.