Littafi Mai Tsarki

1 Yah 5:5-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Wane ne yake nasara da duniya, in ba wanda ya gaskata Yesu Ɗan Allah ba ne?

6. Shi ne wanda ya bayyana ta wurin ruwa da jini, Yesu Almasihu, ba fa ta wurin ruwa kaɗai ba, amma ta wurin ruwa da jini.

7. Ruhu kuma shi ne mai ba da shaida, domin Ruhun shi ne gaskiya.

8. Akwai shaidu uku, wato Ruhun, da ruwa, da kuma jini, waɗannan uku kuwa manufarsu ɗaya ce.

9. Tun da yake muna yarda da shaida mutane, ai, shaidar Allah ta fi ƙarfi. Wannan ita ce shaidar Allah, wato, ya shaidi Ɗansa.

10. Kowa ya gaskata da Ɗan Allah, shaidar tana nan gare shi. Wanda bai gaskata Allah ba, ya ƙaryata shi ke nan, domin bai gaskata shaidar da Allah ya yi Ɗansa ba.

11. Wannan kuma ita ce shaidar, cewa Allah yā ba mu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Ɗansa.

12. Duk wanda yake da Ɗan, yana da rai. Wanda ba shi da Ɗan Allah kuwa, ba shi da rai.