Littafi Mai Tsarki

1 Bit 1:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Daga Bitrus, manzon Yesu Almasihu, zuwa ga zaɓaɓɓun Allah da suke bare, a warwatse a Fantas, da Galatiya, da Kafadokiya, da Asiya, da kuma Bitiniya,

2. su da suke zaɓaɓɓu bisa ga rigyasanin Allah Uba, waɗanda Ruhu kuma ya tsarkake, domin su yi wa Yesu Almasihu biyayya, su kuma tsarkaka da jininsa. Alheri da salama su yawaita a gare ku.

3. Godiya ta tabbata a gare shi, shi wanda yake Allah da Uba na Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ta wurin tsananin jinƙansa ya sāke haifuwarmu, domin mu yi rayayyen bege, ta wurin albarkacin tashin Yesu Almasihu daga matattu,

4. mu kuma sami gādo marar lalacewa, marar ɓāci, marar ƙarewa kuma, wanda aka keɓe muku a Sama,

5. wato, ku da ikon Allah yake kiyayewa ta wurin bangaskiyarku, domin samun ceton nan da aka shirya a bayyana a ƙarshen zamani.

6. A kan wannan ne kuke da matuƙar farin ciki, ko da yake da ɗan lokaci kwa yi baƙin ciki ta dalilin gwaje-gwaje iri iri.