Duk waɗanda suka fake gare ka za su yi farin ciki,Kullum za su yi ta raira waƙa domin murna.Kana kiyaye waɗanda suke ƙaunarka,Suna kuwa matuƙar murna saboda kai.