Littafi Mai Tsarki

Zab 41 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Addu'ar Roƙon Warkewa

1. Mai farin ciki ne wanda yake kula da matalauta,Ubangiji zai taimake shi sa'ad da yake shan wahala.

2. Ubangiji zai kiyaye shi, yă keɓe ransa.Ubangiji zai sa yă ji daɗi a ƙasar,Ba zai bar shi a hannun magabtansa ba.

3. Ubangiji zai taimake shi sa'ad da yake ciwoYa mayar masa da lafiyarsa.

4. Na ce, “Na yi maka zunubi, ya Ubangiji,Ka yi mini jinƙai ka warkar da ni!”

5. Magabtana suna mugayen maganganu a kaina,Suna cewa, “Yaushe ne zai mutu a manta da shi?”

6. Masu zuwa su gaishe ni ba da zuciya ɗaya suke zuwa ba,Sukan tattara duk mugun labari a kainaSa'an nan su je su yi ta bazawa ko'ina.

7. Maƙiyana duk suna raɗa da junansu a kaina,Sukan ɗauka na fi kowa mugunta.

8. Suna cewa, “Yana ciwon ajali,Ba zai taɓa tashi daga gadonsa ba.”

9. Har da shaƙiƙin abokina,Wanda na fi amincewa da shi.Wanda muke ci tare, ya juya yana gāba da ni.

10. Ka ji ƙaina ya Ubangiji, ka maido mini da lafiyata,Zan kuwa sāka wa magabtana!

11. Zan sani kana jin daɗina,Domin ba za su rinjaye ni ba,

12. Za ka taimake ni domin ina yin abin da yake daidai,Za ka sa ni a gabanka har abada.