Littafi Mai Tsarki

Zab 32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Albarkar Gafarar Zunubi

1. Mai farin ciki ne mutumin da aka gafarta masa zunubansa,Mai farin ciki ne kuma wanda aka gafarta masa laifofinsa.

2. Mai farin ciki ne wanda Ubangiji bai zarge shi a kan wani laifi ba,Wanda ba algus ko kaɗan a cikinsa.

3. Sa'ad da ban hurta zunubaina ba,Na gajiyar da kaina da yawan kuka dukan yini.

4. Ka hukunta ni dare da rana, ya Ubangiji,Ƙarfina duka ya ƙare sarai,Kamar yadda laima yake bushewa,Saboda zafin bazara.

5. Sa'an nan na hurta zunubaina gare ka,Ban ɓoye laifofina ba.Na ƙudurta in hurta su gare ka,Ka kuwa gafarta dukan laifofina.

6. Saboda haka dukan jama'arka masu biyayya,Za su yi addu'a gare ka, lokacin bukata.Sa'ad da babbar rigyawa ta malalo,Ba za ta kai wurinsu ba.

7. Kai ne maɓoyata,Za ka cece ni daga wahala.Ina raira waƙa da ƙarfi saboda cetonka,Domin ka kiyaye ni.

8. Ubangiji ya ce, “Zan koya maka hanyar da za ka bi,Zan koya maka, in kuma ba ka shawara.

9. Kada ka zama wawa kamar doki ko alfadari,Wanda dole sai da linzami, da ragama za a sarrafa shi,Sa'an nan yă yi maka biyayya.”

10. Tilas ne mugu yă sha wahala,Amma masu dogara ga Ubangiji,Madawwamiyar ƙaunarsa tana kiyaye su.

11. Dukanku adalai, ku yi murna,Ku yi farin ciki,Saboda abin da Ubangiji ya yi!Dukanku da kuke yi masa biyayya,Ku yi sowa ta farin ciki!