Littafi Mai Tsarki

Zab 141 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Addu'ar Maraice ta Neman Keɓewa daga Mugunta

1. Ina kira gare ka, ya Ubangiji,Ka taimake ni yanzu!Ka saurare ni sa'ad da na kira gare ka.

2. Ka karɓi addu'ata kamar turaren ƙonawa,Ka karɓi ɗaga hannuwa sama da na yi kamar hadayar maraice.

3. Ya Ubangiji, ka sa a yi tsaron bakina,Ka sa mai tsaro a leɓunana.

4. Ka tsare ni daga son yin mugunta,Ko kuma in haɗa kai da mugaye cikin muguntarsu,Ka sa kada in taɓa yin tarayya da su a bukukuwansu!

5. Nagarin mutum ya iya hukunta ni, ya tsauta mini da alheri,Zai zamar mini kamar an shafe kaina da mai,Domin kullayaumi ina addu'a gāba da mugayen ayyuka.

6. Mutane za su yarda, cewa maganata gaskiya ce,Sa'ad da aka jefo da masu mulkinsu ƙasa, daga ƙwanƙolin dutse,

7. Kamar itacen da aka faskare, aka daddatse,Haka aka watsar da ƙasusuwansu a gefen kabari.

8. Amma ni, ya Ubangiji Allah, da nake dogara a gare ka,Ina neman kiyayewarka,Kada ka bar ni in halaka!

9. Ka kiyaye ni daga tarkunan da suka kafa mini,Daga ashiftar masu aikata mugunta.

10. Ka sa mugaye su fāɗa cikin tarkunansu,Ni kuwa in zo in wuce lafiya.