Littafi Mai Tsarki

Zab 128 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Albarkar Mai Tsoron Ubangiji

1. Mai farin ciki ne wanda yake tsoron Ubangiji,Wanda yake zamansa bisa ga umarnansa!

2. Za ka sami isasshen abin biyan bukatarka,Za ka yi farin ciki ka arzuta.

3. Matarka za ta zama kamar kurangar inabiMai 'ya'ya a gidanka,'Ya'yanka maza kuma kamar dashen zaitunSuna kewaye da teburinka.

4. Mutumin da yake yi wa Ubangiji biyayya,Hakika za a sa masa albarka kamar haka.

5. Ubangiji ya sa maka albarka daga Sihiyona!Ya sa ka ga Urushalima ta arzutaDukan kwanakinka!

6. Ya kuma sa ka ka ga jikokinka!Salama ta kasance ga Isra'ila!