Littafi Mai Tsarki

Zab 123 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Addu'ar Neman Jinƙai

1. Ya Ubangiji, ina zuba ido gare ka,A Sama inda kake mulki.

2. Kamar yadda bara yake dogara ga maigidansa,Baranya kuma ga uwargijiyarta,Haka nan muke zuba ido gare ka, ya Ubangiji Allahnmu,Har mu sami jinƙanka.

3. Ka yi mana jinƙai, ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai,An gwada mana wulakanci matuƙa!

4. Attajirai sun daɗe suna ta yi mana ba'a,Azzalumai masu girmankai sun raina mu!