Littafi Mai Tsarki

Zab 101 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Alkawarin Sarki domin Zaman Adalci

1. Waƙata ta aminci ce da gaskiya.Ina raira maka ita, ya Ubangiji.

2. Abin da nake yi ba zai zama laifi ba,Yaushe za ka zo wurina?Da zuciya mai tsabta zan zauna a gidana.

3. Ba zan jure da mugunta ba ko kaɗan.Na ƙi jinin ayyukan waɗanda suka bijire wa Allah,Ba ruwana da su.

4. Ba zan yi rashin aminci ba,Ba kuwa zan yi tunanin mugunta ba.

5. Zan hallakar da mai raɗar abokinsa,Ba zan jure da mutum mai girmankai,Ko mai alfarma ba.

6. Zan yarda da waɗanda suke amincewa da Allah,Zan yardar musu si yi zamansu a fādata,Zan yarda wa waɗanda suke da tabbataccen aminciSu yi mini hidima.

7. Maƙaryaci ba zai zauna a fādata ba,Ba zan yarda munafuki ya yi zamansa a wurina ba.

8. A kowace rana zan yi ta karkashe dukan mugayen da suke cikin ƙasarmu,Zan kori dukan mugaye daga birnin Ubangiji.