Ya kuwa yardar musu. Sai baƙaƙen aljannun suka fita, suka shiga aladun. Garken kuwa wajen alade dubu biyu, suka rugungunto ta gangaren, suka fāɗa tekun, suka halaka a ruwa.