Gidiyon ya kama wani saurayi na Sukkot, ya yi masa tambayoyi. Shi kuwa ya rubuta masa sunayen sarakuna da na dattawan Sukkot, mutum saba'in da bakwai.