Dukan wanda ya ga haka sai ya ce, “Ba mu taɓa ganin irin wannan abu ba, ba a kuwa taɓa yin haka ba tun daga ranar da Isra'ilawa suka fito daga ƙasar Masar sai yau. Ku yi tunani, me za mu yi a kan wannan al'amari?”