Amma Samson ya yi kwanciyarsa har tsakar dare. Sa'an nan ya tashi ya kama ƙyauren ƙofar birnin, da madogarai biyu na ƙofar, ya tumɓuke su. Ya saɓe su a kafaɗarsa, ya kai su kan dutsen da yake a gaban Hebron.