Ubangiji Allah na Isra'ila kuwa ya ba da Sihon da mutanensa duka ga Isra'ilawa, suka ci su da yaƙi. Suka kuwa mallaki dukan ƙasar Amoriyawa da mazaunan ƙasar.